ad-Dukhan (الدُّخَان)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 44 • 59 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
44:1 Ḥ. M̃.
44:2 Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
44:3 Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.
44:4 A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.
44:5 Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.
44:6 Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.
44:7 (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).
44:8 Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
44:9 A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.
44:10 Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.
44:11 Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.
44:12 Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.
44:13 Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?
44:14 Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."
44:15 Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).
44:16 Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.
44:17 Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.
44:18 (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."
44:19 "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."
44:20 "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."
44:21 "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."
44:22 Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.
44:23 (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"
44:24 "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."
44:25 Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.
44:26 Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.
44:27 Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.
44:28 Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.
44:29 Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
44:30 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.
44:31 Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.
44:32 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.
44:33 Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna
44:34 Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,
44:35 "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
44:36 "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
44:37 shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.
44:38 Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.
44:39 Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.
44:40 Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.
44:41 Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.
44:42 fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
44:43 Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),
44:44 Ita ce abincin mai laifi.
44:45 Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.
44:46 Kamar tafasar ruwan zãfi.
44:47 (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."
44:48 "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."
44:49 (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"
44:50 "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."
44:51 Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.
44:52 A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.
44:53 Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.
44:54 Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.
44:55 Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).
44:56 Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.
44:57 Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
44:58 Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.
44:59 Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.