77:1
Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
77:2
Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
77:3
Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
77:4
sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
77:5
Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
77:6
Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
77:7
Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
77:8
To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
77:9
Kuma, idan sama aka tsãge ta.
77:10
Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
77:11
Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
77:12
Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
77:13
Domin rãnar rarrabẽwa.
77:14
Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
77:15
Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:16
Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
77:17
Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
77:18
Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
77:19
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
77:20
Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
77:21
Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
77:22
Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
77:23
Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
77:24
Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
77:25
Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
77:26
Ga rãyayyu da matattu,
77:27
Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
77:28
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:29
Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
77:30
Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
77:31
Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
77:32
Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
77:33
Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
77:34
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:35
Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
77:36
Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
77:37
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:38
Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
77:39
To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
77:40
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:41
Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
77:42
Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
77:43
(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
77:44
Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
77:45
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:46
(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
77:47
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:48
Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
77:49
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:50
To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni