adh-Dhariyat (الذَّارِيَات)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 51 • 60 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
51:1 Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
51:2 Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
51:3 Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.
51:4 Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).
51:5 Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
51:6 Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne
51:7 Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo).
51:8 Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani).
51:9 Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).
51:10 An la'ani mãsu ƙiri-faɗi.
51:11 Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.
51:12 Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"
51:13 Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.
51:14 (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."
51:15 Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.
51:16 Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).
51:17 Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.
51:18 Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.
51:19 Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.
51:20 Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.
51:21 Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?
51:22 Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.
51:23 To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,
51:24 Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
51:25 A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!"
51:26 Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,
51:27 Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?"
51:28 Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.
51:29 Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!"
51:30 Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi."
51:31 (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"
51:32 Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
51:33 "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).
51:34 "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."
51:35 Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
51:36 Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
51:37 Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
51:38 Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.
51:39 Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"
51:40 Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
51:41 Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
51:42 Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
51:43 Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"
51:44 Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
51:45 Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.
51:46 Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
51:47 Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
51:48 Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
51:49 Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
51:50 Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
51:51 Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
51:52 Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
51:53 shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
51:54 Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
51:55 Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
51:56 Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
51:57 Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.
51:58 Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
51:59 To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
51:60 Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.