Qaf (ق)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 50 • 45 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
50:1 ¡̃. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.
50:2 Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."
50:3 "Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."
50:4 Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.
50:5 Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.
50:6 Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
50:7 Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?
50:8 Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
50:9 Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
50:10 Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
50:11 Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.
50:12 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, da Samũdãwa.
50:13 Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
50:14 Da ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
50:15 Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.
50:16 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa.
50:17 A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.
50:18 Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
50:19 Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
50:20 Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
50:21 Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
50:22 (Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
50:23 Kuma abõkin haɗinsa ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
50:24 (A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."
50:25 "Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
50:26 "Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."
50:27 Abõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
50:28 Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
50:29 "Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa."
50:30 Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani ƙãri?"
50:31 Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
50:32 "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
50:33 "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."
50:34 (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama."
50:35 Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
50:36 Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? (Babu).
50:37 Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
50:38 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
50:39 Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
50:40 Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
50:41 Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci.
50:42 Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
50:43 Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
50:44 Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
50:45 Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.