75:1
Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.
75:2
Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.
75:3
Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
75:4
Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
75:5
Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
75:6
Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"
75:7
To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
75:8
Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
75:9
Aka tãra rãnã da watã
75:10
Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
75:11
A'aha! bãbu mafaka.
75:12
zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
75:13
Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
75:14
Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
75:15
Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
75:16
Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
75:17
Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
75:18
To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
75:19
sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
75:20
A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
75:21
Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
75:22
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
75:23
Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
75:24
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
75:25
Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
75:26
A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
75:27
kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
75:28
Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
75:29
Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
75:30
Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
75:31
To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
75:32
Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
75:33
Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
75:34
Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
75:35
Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
75:36
Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
75:37
Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
75:38
Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
75:39
Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
75:40
Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?