an-Nazi`at (النَّازِعَات)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 79 • 46 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
79:1 Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
79:2 Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
79:3 Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
79:4 Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.
79:5 Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
79:6 Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
79:7 Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
79:8 Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
79:9 Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
79:10 Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
79:11 "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"
79:12 Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"
79:13 To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
79:14 Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
79:15 Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
79:16 A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?
79:17 Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.
79:18 "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.
79:19 "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"
79:20 Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.
79:21 Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),
79:22 Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.
79:23 Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.
79:24 Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."
79:25 Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.
79:26 Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.
79:27 Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
79:28 Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.
79:29 Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
79:30 Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.
79:31 Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.
79:32 Da duwatsu, Yã kafe ta.
79:33 Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.
79:34 To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.
79:35 Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.
79:36 Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.
79:37 To, amma wanda ya yi girman kai.
79:38 Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).
79:39 To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.
79:40 Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
79:41 To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.
79:42 Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?
79:43 Me ya haɗã ka da ambatonta?
79:44 Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.
79:45 Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.
79:46 Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.