`Abasa (عَبَسَ)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 80 • 42 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
80:1 Yã game huska kuma ya jũya bãya.
80:2 Sabõda makãho yã je masa.
80:3 To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.
80:4 Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
80:5 Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.
80:6 Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
80:7 To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
80:8 Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
80:9 Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
80:10 Kai kuma kã shagala ga barinsa!
80:11 A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
80:12 Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
80:13 (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
80:14 Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.
80:15 A cikin hannãyen mala'iku marubũta.
80:16 Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.
80:17 An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!
80:18 Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
80:19 Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
80:20 Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
80:21 Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
80:22 Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
80:23 Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
80:24 To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
80:25 Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
80:26 Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
80:27 Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.
80:28 Da inabi da ciyãwa.
80:29 Da zaitũni da itãcen dabĩno.
80:30 Da lambuna, mãsu yawan itãce.
80:31 Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
80:32 Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
80:33 To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
80:34 Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.
80:35 Da uwarsa da ubansa.
80:36 Da mãtarsa da ɗiyansa.
80:37 Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.
80:38 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
80:39 Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
80:40 Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.
80:41 Baƙi zai rufe su.
80:42 Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).