al-Mutaffifin (المُطَفِّفِين)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 83 • 36 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
83:1 Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
83:2 Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
83:3 Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa
83:4 Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
83:5 Domin yini mai girma.
83:6 Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
83:7 Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
83:8 Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
83:9 Wani 1ittãfi ne rubũtacce.
83:10 Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
83:11 Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
83:12 Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
83:13 Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
83:14 A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
83:15 A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
83:16 Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
83:17 Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
83:18 A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
83:19 Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
83:20 Wani littãfi ne rubũtacce.
83:21 Muƙarrabai suke halarta shi.
83:22 Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
83:23 A kan karagu, suna ta kallo.
83:24 Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
83:25 Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
83:26 ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
83:27 Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
83:28 (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
83:29 Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
83:30 Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
83:31 Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
83:32 Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
83:33 Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
83:34 To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
83:35 A kan karagu, suna ta kallo.
83:36 Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?