88:1
Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
88:2
Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
88:3
Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
88:4
Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
88:5
Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
88:6
Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
88:7
Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
88:8
Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
88:9
Game da aikinsu, masu yarda ne.
88:10
(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
88:11
Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
88:12
A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
88:13
A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
88:14
Da kõfuna ar'aje.
88:15
Da filõli jẽre,
88:16
Da katifu shimfiɗe.
88:17
Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
88:18
Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
88:19
Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
88:20
Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
88:21
sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
88:22
Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
88:23
Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
88:24
To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
88:25
Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
88:26
Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.