92:1
Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
92:2
Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
92:3
Da abin da ya halitta namiji da mace.
92:4
Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
92:5
To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
92:6
Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo.
92:7
To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
92:8
Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
92:9
Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
92:10
To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
92:11
Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
92:12
Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
92:13
Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
92:14
Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
92:15
Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
92:16
Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
92:17
Kuma mafi taƙawa zai nisance ta.
92:18
Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
92:19
Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
92:20
Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
92:21
To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).