91:1
Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.
91:2
Kuma da wata idan ya bi ta.
91:3
Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.
91:4
Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
91:5
Da sama da abin da ya gina ta.
91:6
Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
91:7
Da rai da abin da ya daidaita shi.
91:8
Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.
91:9
Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.
91:10
Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.
91:11
Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.
91:12
A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).
91:13
Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"
91:14
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).
91:15
Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).