ad-Dhuha (الضُّحَىٰ)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 93 • 11 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
93:1 Inã rantsuwa da hantsi.
93:2 Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
93:3 Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
93:4 Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
93:5 Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
93:6 Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
93:7 Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
93:8 Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
93:9 Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
93:10 Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
93:11 Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).