al-`Alaq (العَلَق)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 96 • 19 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
96:1 Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
96:2 Ya hahitta mutum daga gudan jini.
96:3 Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
96:4 Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
96:5 Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
96:6 A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
96:7 Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
96:8 Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
96:9 Shin, kã ga wanda ke hana.
96:10 Bãwã idan yã yi salla?
96:11 Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
96:12 Ko ya yi umurni da taƙawa?
96:13 Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
96:14 Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
96:15 A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
96:16 Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
96:17 Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
96:18 Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).
96:19 A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).