al-Qadr (القَدْر)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 97 • 5 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
97:1 Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)
97:2 To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari?
97:3 Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
97:4 Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.
97:5 Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.