at-Tariq (الطَّارِق)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 86 • 17 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
86:1 Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
86:2 To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
86:3 Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.
86:4 Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
86:5 To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
86:6 An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
86:7 Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
86:8 Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
86:9 Rãnar da ake jarrabawar asirai.
86:10 Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
86:11 Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
86:12 Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,
86:13 Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki
86:14 Kuma shĩ bã bananci bane
86:15 Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
86:16 Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
86:17 Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.