Nuh (نُوح)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 71 • 28 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
71:1 Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
71:2 Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
71:3 "Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni."
71:4 "Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
71:5 Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
71:6 "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
71:7 "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai."
71:8 "Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
71:9 "Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
71:10 "Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."
71:11 "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga."
71:12 "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna."
71:13 "Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,"
71:14 "Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?"
71:15 "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?"
71:16 "Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?"
71:17 "Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa."
71:18 "Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa."
71:19 "Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya."
71:20 "Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi."
71:21 Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra."
71:22 "Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba."
71:23 "Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra."
71:24 "Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata."
71:25 Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
71:26 Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida."
71:27 "Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci"
71:28 "Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka."