al-Qari`ah (القَارِعَة)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 101 • 11 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
101:1 Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
101:2 Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
101:3 Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
101:4 Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
101:5 Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
101:6 To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
101:7 To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
101:8 Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
101:9 To, uwarsa Hãwiya ce.
101:10 Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
101:11 Wata wuta ce mai zafi.