at-Takathur (التَّكَاثُر)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 102 • 8 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
102:1 Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).
102:2 Har kuka ziyarci kaburbura.
102:3 A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.
102:4 Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.
102:5 Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
102:6 Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
102:7 Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
102:8 Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).