al-`Asr (العَصْر)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 103 • 3 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
103:1 Ina rantsuwa da zãmani.
103:2 Lalle ne mutum yana a cikin hasara.
103:3 Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara).