al-Humazah (الهُمَزَة)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 104 • 9 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
104:1 Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
104:2 Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
104:3 Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
104:4 A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
104:5 Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
104:6 Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
104:7 Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
104:8 Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.
104:9 A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.