al-Fil (الفِيل)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 105 • 5 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
105:1 Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba?
105:2 Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
105:3 Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
105:4 Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
105:5 Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?