al-Falaq (الفَلَق)

Abubakar Mahmoud Gumi by Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 113 • 5 verses • Meccan

113:1 Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"
113:2 "Daga sharrin abin da Ya halitta."
113:3 "Da sharrin dare, idan ya yi duhu."
113:4 "Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin ƙulle-ƙulle."
113:5 "Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada."