al-Ma`un (المَاعُون)

Abubakar Mahmoud Gumi by Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 107 • 7 verses • Meccan

107:1 Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
107:2 To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa).
107:3 Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
107:4 To, bone yã tabbata ga masallata.
107:5 Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu.
107:6 Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu)
107:7 Kuma suna hana taimako.