al-Kauthar (الكَوْثَر)

Abubakar Mahmoud Gumi - Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 108 • 3 verses • Meccan

← Previous Chapter Next Chapter →
108:1 Lalle ne Mu, Mun yi maka kyauta mai yawa.
108:2 Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi).
108:3 Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka.